✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wadanda suka sace Dan Majalisa da daliban ABU a Kaduna

‎Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama masu garkuwa da mutane 25 ciki har da wadanda suka sace Dan majalisar Dokokin jihar Sulaiman Ibrahim Dabo…

‎Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama masu garkuwa da mutane 25 ciki har da wadanda suka sace Dan majalisar Dokokin jihar Sulaiman Ibrahim Dabo a kwanakin baya.

Rundunar ta ‘Yan Sanda ta kuma bayyana cewa cikin wadanda aka kama harda wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Ahmadu Bello Zaria.

A cikin wata Sanarwa da kakakin Rundunar Yakubu Sabo, ya fitar ya ce rundunar ta kuma yi nasarar hallaka wasu yan ta’adda uku a yayin wani samame da suka kai mafakarsu.

Ya ce, daya daga cikin wadanda aka kamma sun bayyana cewa su ne suke addabar matafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Zariya.

Yakubu, ‎ya ce jami’an su sun kuma kai wani samame yankin Kingimi da Sauran kauyuka a karamar Hukumar Igabi, a inda suka kama wani katsungumin mai garkuwa da mutane mai suna Buhari Bello mai shekaru 34 da wasu mutum bakwai .

Ya ce, a yayin bincike ne suka bada bayanai da ya yi sanadiyyar kama sauran abokanen barnar su.