Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero ya fada komar ’yan sanda a Owerri, babban birnin Jihar Imo.
Rahotanni sun ce ’yan sanda dauke da makamai ne suka kama Ajaero a Sakatariyar ƙungiyar NLC a Owerri, lokacin da yake shirin jagorantar wata zanga-zanga da aka shirya gudanarwa a yau.
- Babu laifi don uba da ɗansa sun samu saɓani — Fubara
- Kotu ta yanke wa wanda ya watsa wa budurwarsa ruwan batir daurin rai da rai
Babban jami’in hulda da jama’a da harkokin sadarwa na NLC, kwamared Benson Uper ya tabbatar da rahoton kama Joe Ajaero cikin wani sako da ya aike wa Gidan Talbijin na Channels..
Ya ƙara da cewa mutanen da suka kama jagoran ’yan ƙwadagon na Najeriya sun je ne da kakin ƴan sanda inda suka yi awon gaba da shi.
Kungiyar NLC na jagorantar zanga-zanga da yajin aiki a jihar Imo saboda abin da ta bayyana, a matsayin rashin mutunta haƙƙin ma’aikata da rashin biyan albashi da fansho da dai sauransu.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Imo Okoye Henry ya fitar, ta ce mafaka ta bai wa shugaban na NLC sabanin jita-jitar cewa kama shi ta yi.
Sanarwar ta ce wannan na zuwa ne yayin da aka samu sa’insa da wasu ma’aikata a filin jirgin sama da ke Owerri, inda suka kai wa shugaban na NLC hari a kokarinsu na ƙin bai wa zanga-zangar hadin kai.
Mista Henry ya ce yanzu haka ma shugaban ’yan ƙwadagon yana samun kulawa a Asibitin ’Yan sanda da ke Owerri.