✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mutane 32 da suka tayar da hargitsi a coci

’Yan sanda a Jihar Kwara sun kama mutane 32 da suka tayar da hargitsi a cikin tsakar daren jajibirin sabuwar shekara ta 2018 a garin…

’Yan sanda a Jihar Kwara sun kama mutane 32 da suka tayar da hargitsi a cikin tsakar daren jajibirin sabuwar shekara ta 2018 a garin Ilorin.

Gungun matasan sun shiga cikin majami’un Catholic da Methodist da wurin ibadar Musulmi na makarantar sakandare ta United Secondary School, duka a garin Ilorin, inda suka lalata kayayyaki a ciki da wajen mujami’un tare da kwace kudade daga hannun masu ibada.

Duka wannan al’amari ya auku ne a Unguwar Ibrahim Taiwo Isale, a garin Ilorin a inda wasu masu ibada suka samu raunuka a dalilin gudun tsira da suka yi. An lalata motoci da kayayyaki na cikin wuraren ibadar.

Da yake yi wa Aminiya karin haske a kan wannan al’amari, Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Kwara, Alhaji Lawan Ado ya ce wasu bata-garin matasa ne dauke da makamai suka haddasa hargitsin ta fannin auka wa majami’un Catholic da Methodist da ke kusa da juna da makarantar United Secondary School, a inda Musulmi mabiya darikar kuareeb da masu ibadar addinin Kirista suke yin bauta da addu’o’i a cikin tsakiyar daren ranar Lahadi wato ranar jajibirin sabuwar shekarar da muke ciki.

Kwamishinan ’yan sandan wanda shi da kansa ya jagoranci tawagar jami’an da suka tarwatsa wadannan matasa tare da kama su a cikin daren, ya ja kunnen masu danganta al’amarin da rikicin addini su daina yada irin wannan jita-jitar, “domin babu abun da ya hada hargitsin da addini.”

Ya yi kira ga jama’a mazauna birnin Ilorin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin tuni ’yan sanda suka shawo kan al’amarin. Ya ce, da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadannan matasa ne gaban kuliya domin yanke masu hukumci.

Gwamna Abdulfatah Ahmed na Jihar Kwara ya nuna matukar bakin ciki dangane da aukuwar wannan al’amari, wanda ya ce sabon abu ne da miyagun mutane suka fito da shi a jihar. Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk abun da take iyawa wajen kare lafiya da dukiyar jama’a domin samar da zama lafiya a jihar. Gwamnan ya jinjina wa matakin da wasu mutane suka dauka na yin kariya ga masu ibada a cikin daren ba tare da nuna banbancin addini ba.