✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama matashin da ya harbi mutum 8 a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai suna Musa Uba Muhammad, dan wani babban dan siyasa a jihar, Alhaji Uba…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai suna Musa Uba Muhammad, dan wani babban dan siyasa a jihar, Alhaji Uba Danbayye sakamakon zarginsa da laifin harbin mutum takwas a garin Ajingi da ke Jihar Kano.

Rahotanni sun ce lokacin da ake kirga kuri’a ne matasan yankin wadanda ake zargin ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka fara murnar cin zabe a yankin har ma suka biyo ta kofar gidan su Musa suna ihun samun nasara, lamarin da ya fusata matashin ya dauko bindiga ya fara harbin kan mai uwa da wabi.

A lokacin da wanda ake zargin ya bude wuta a kan matasan ne wani yaro mai suna Muhammad Umar ya rasa ransa sakamakon harsashi da ya huda cikinsa yayin da wadansu mutum takwas suka samu raunuka.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan  Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce jami’ansu da ke ofishin ’yan sanda na garin Ajingi suka kama matashin, inda kuma a halin yanzu yake a sashen da ke kula da manyan laifuffuka na rundunar.

“Wadanda aka harba an kai su asibiti, inda har an sallami wadansu daga cikinsu; yayin da ragowar suke jinya a asibiti,” inji shi.

DSP Kiyawa ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike za ta gurfanar da Musa Uba Muhammad gaban kotu domin yi masa shari’a.