✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kaddamar da kamfen din ‘Beli kyauta ne’

A kokarin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano na magance cin hanci da rashawa a tsakanin jami’anta, rundunar ta kaddamar da kamfe din wayar da kan…

A kokarin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano na magance cin hanci da rashawa a tsakanin jami’anta, rundunar ta kaddamar da kamfe din wayar da kan jama’a mai take da “Beli Kyauta.” 

Da yake yi wa manema labarai karin haske a kan gangamin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Rabi’u Yusuf  ya ce makasudin gangamin shi ne don ilimintar da jama’a cewa beli kyauta ne, kada wani ya bayar da ko kwabo don neman beli daga ’yan sanda.

Kwamishina Rabi’u Yusuf ya ce gangamin ya yi daidai da yakin da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ke yi domin magance cin hanci a tsakanin ’yan sanda.

Kwamishiiman ya yi kira ga jama’ar jihar su daina biyan ko kwabo wajen neman belin ’yan uwansu daga ’yan sanda kuma su kai rahoton duk dan sandan da ya nemi su bayar da kudin beli ga ofishin ’yan sandan da ya dace.

Kwamishinan ya gargadi ’yan sanda cewa duk dan sandan da aka kama yana karbar kudi da sunan beli ko wani abu a matsayin cin hanci zai dandana kudarsa. “Lokaci ya yi da ’yan sanda za su fahimci cewa cin hanci ba abin burgewa ba ne. Ya kamata ’yan sandan su zama wakilan samar da canji amma ba su zama masu kawo tarnaki ga canjin da ake fafutikar samarwa a kasar nan ba. Ya kamata ’yan sanda su rika gudanar da ayyukansu yadda doka ta tanada,” inji shi.