Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bada umarnin haramta zanga-zanga a faɗin jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Useni Gumel ne ya bada umarnin da safiyar Litinin.
Hakan ya biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano da jam’iyyar adawa ta APC.
Sai dai duk da haka an gudanar da zanga-zangar kuma an ƙare lami lafiya.