✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun fatattaki ‘yan bindiga a Abuja

Rundunar ta jadadda aniyar samar sa tsaro a fadin Najeriya.

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga a sansaninsu da ke unguwar Mpape, a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce an kai samamen ne a ranar 9 ga watan Fabrairu bayan samun bayanan sirri.

Ya ce, sun yi nasarar kashe wasu kasurguman mahara a maboyar.

Ya ce sun hallaka kasurgumin dan bindigar da ya addabi yankunan Mpape, Bwari a Abuja, Kagarko a Kaduna, Masaka da kuma kauyen Nukun a Jihar Nasarawa.

A cewarsa, maharan sun jima suna satar mutane tare da karbar kudin fansa.

Kazalika, ya ce sun samu nasarar kai farmakin ne a maboyarsu da ke wani tsauni a Mpape tare da kwato makamai.

Adejobi, ya ce sun kwato makamai da suka hada da wayoyin hannu, layin waya, laya da kuma kwayoyi.

Ragowar sun hada da alburusai, adda, wukake da sauran muggan makamai.

Adejobi, ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Ya ce, rundunar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kama masu laifi, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.