Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta kama wani da ake zargin dan fashi ne daga kasar waje a Damasak, a Karamar Hukumar Mobar ta jihar.
Kazalika an damke wani tubabben dan Boko Haram, Baba-Goni Mohammed Ibrahim kan satar dukiyar da ta kai ta 170,000 a Maiduguri.
- Matar da ta huda cikin karamar yarinya da wuka a Kano ta shiga hannu
- ‘Tsarin shiyya-shiyya barazana ce ga cin gashin-kan Majalisa’
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamishinan ’yan sandan jihar, Abdu Umar, ya ce mutanen biyu na cikin mutane 110 da ake zargi da aikata laifuka 70 a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai, Modu Adamu, wanda ke sanye da kayan sojan Nijar, ya bayyana cewa shi dan asalin garin Diffa ne a Jamhuriyar Nijar.
Adamu wanda ya amsa cewar yana da hannu a ayyukan fashi daban-daban guda uku a yankunan, ya ce asirinsu ya tonu ne bayan da suka yi arangama da jami’an tsaron da ta tarwatsa kungiyarsu.
“A aikinmu na farko an ba ni Naira 130,000, sannan Naira 50,000 da Naira 10,000 a aiki na biyu da na uku, amma a karo na hudu mun tare hanya, kwatsam sai muka hangi ‘yan sanda.
“A kokarinmu na tserewa, an kama ni da sauran ‘yan kungiyarmu mutum biyar, Abdu, Kado, Bazamfare, Baida, Bororoji da Umaru.” in ji shi.
Ya bayyana cewa suna sayen bindigar AK47 kan kudi Naira 700,000 a Jamhuriyar Nijar.
Abdu ya ce, kafin ya shiga kungiyar, yana kiwon shanun mahaifinsa a Diffa da Damasak, kuma “Na yi nadamar abin da na yi, har yanzu mahaifina da matata ba su san abin da nake yi ba, ina rokon sassauci”.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, tubabben dan Boko Haram, Baba-Goni, ya ce an kama shi ne da laifin satar atamfa guda takwas da wasu kaya na wata Hajiya Lami a garin Maiduguri.
Ya ce matar ta dauke shi aiki ne a matsayin ma’aikacin gida, amma “Na yi mata aiki tsawon watanni amma ba ta taba biya na ko na wata daya ba; don haka sai na sace mata kaya a matsayin diyya na albashin da ba a biya ni ba.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa wadanda ake zargin su 110 an aka kama su ne kan aikata laifuka daban-daban da suka hada da kisan kai, fashi da makami, fyade, kwace wayar hannu da kuma garkuwa da mutane.
Kwamishinan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.