’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe.
An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin.
- Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe
- Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
DSP Buhari ya tabbatar wa jama’a cewa za a ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ayyukan laifi a jihar.
Sanarwar ta kuma gode wa jama’a bisa haɗin kansu tare da yin kira da su kasance masu sa ido, su kuma riƙa sanar da hukuma game da duk wani abu da suka ga ya dace ko ya saɓa da al’ada a cikin al’umma.