Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutum uku da suka fitini unguwar Kurna Tudun Fulani, da ke garin Kano.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da manema labarai game da cafke matasan da ’yan sanda suka yi a ranar 8 ga watan Fabrairu 2022.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Harshen Koyarwa Kan Neman Ilimi
- Kannywood ta dauki zafi kan maganar biyan hakkin ’yan wasa
- Na biya Ladin Cima N40,000 a fim din Gidan Badamasi —Nazir Salihi
Matasan sun shiga hannu ne a lokuta daban-daban; a unguwar Dan Rimi da unguwar Zage tsakanin ranar 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu.
Kiyawa, ya ce tuni wadanda ake zargin suka amsa tuhumar da ake musu na aikata manyan laifuka a unguwar Kurna Tudun Fulani, inda suka raunata mutane da dama.
Ya ce rundunar na gudanar da bincike kan irin miyagun ayyukan da matasan suka tafka don gurfanar da su gaban shari’a.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun addabi unguwanni da dama a cikin Kano, musamman unguwar Kurna Tudun Fulani da ke Karamar Hukumar Ungogo, inda suka raunata mutane da dama.