’Yan sandan sun kama wata mata da wasu maza biyu da suka yi garkuwa da dan mai unguwar Galadanchi, Ado Sunusi a Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
Bayan ’yan sanda sun zurfafa bincike, sun gano motar da aka sace yaron, suka kuma kamo direban motar a titin Beruit, cikin birnin Kano.
- ’Yan kasuwar Kano da aka yi garkuwa da su sun kubuta
- APC ta lashe zaben kananan hukumomin Kano
- Jami’ar Bayero ta wajabta amfani da takunkumin rufe fuska
- Yadda ’yan sanda ke ‘garkuwa da mutane’ a Kano’
Ta hanyarsa ne aka gano maboyar matar wadda ita ce shugabar gungun masu garkuwar da mutanen tare da wasu daga cikin yaranta.
Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta bayyana cewa ta cika hannu da mutanen ne a samamen da jami’anta suka kai maboyar masu garkuar da ke a Unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo.
Ta ce matar da maza uku ne aka kama a gidan, amma biyu daga cikin mazan an tabbatar da ’yan asalin Jihar Zamfara ne.
Bincike ya nuna cewa matar ta kama hayar gidan da suke zaune a Unguar Jaba ne kan N600,000 duk shekara a hannun wani dilalli.
Matar ta fada wa ’yan sanda cewa ta fara garkuwa da mutane ne bayan an kashe mijinta a Jihar Zamfara.