Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da cafke wasu mutum biyu da ake zargi dillalan miyagun kwayoyi ne a Jihar Jigawa.
Kamen na zuwa ne a yayin da DPO din ofishin ’yan sanda na Malam Madori, SP Muhammad Usman ya jagoranci wata tawagar jami’ai wajen cafke dillalan miyagun kwayoyin da suka yi kaurin suna a yankunan da ke karshin Masarautar Hadejia.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Shissu Adam, ya bayyana sunayen ababen zargin biyu da cewar mazauna ne a yankin na Malam Madori.
Shissu ya ce an cimma wannan nasara ce a yayin simamen da tawagar jami’an ta kai maboyar masu ta’adar a kasuwar Malam Madori biyo bayan bayanan sirrin da suka samu.
Daga cikin miyagun kayan mayen da aka samu a hannun mutanen biyu akwai kwayar nan mai sa dogon bacci mai tsanani ta Valium guda 550, kwayar Diazepam guda 60 da kuma dauri 55 na curin wata busasshiyar ciyawa da ke zargi tabar wiwi ce da kwayar Tramadol guda 10 da fakiti daya na takardar Rexler da kuma wata zabira daya.
Babban jami’in ya ce a halin yanzu a na ci gaba da gudanar da bincike a kansu gabanin mika su gaban kotu.