’Yan sandan kasar Isra’ila sun mika wa masu shigar da kara bayanan da suke neman a gurfanar da Firayi Ministan kasar, Mista Benjamin Netanyahu a gaban kotu domin tuhumarsa da cin hanci da rashawa da kuma zamba cikin aminci.
’Yan sandan sun nemi a gurfanar da Firayi Minista Netanyahu ne a kan batutuwa biyu da suka shafi batun karbar kyaututtuka da ya yi domin yi wa wadanda suka ba shi kyautar wani aiki.
’Yan sandan sun ce Benjamin Netanyahu ya rika ba wadansu abokansa ayyuka na musamman bayan ya karbi kaya masu daraja da tsada da suka hada da giyar Champagne da taba sigari da gwala-gwalai.
Na biyu shi ne batun katsalandar da yake yi ga kafafen watsa labarai, inda suka ce Mista Netanyahu ya nemi wata jarida ta fifita shi inda shi kuma ya yi alkawarin dakile wasu jaridu kishiyoyinta.
Sai dai Shugaban na Isra’ila ya yi watsi da matakin na ’yan sanda, inda ya ce, “A shekarun baya an rika neman gurfanar da ni fiye da sau 15 domin a sauke ni daga mukamina. Dukansu sun fara ne da labarai a jarida da talabijin masu cewa na yi manyan laifuffuka.”
Ya kara da cewa, “Wasu ma har da manyan tuhume-tuhume daga ’yan sanda kamar wanna, amma wannan yunkurin ba su yi min komai ba. Saboda na san gaskiya, kuma ina fada muku, a wannan karon ma, babu abin da zai faru.”
Jam’iyyun adawa a Isra’ila sun yi kira ga Mista Netanyahu da ya sauka daga mukaminsa.
Amma a halin yanzu babu wanda ya fi shi tasiri a siyasar kasar.
Za a mika bukatar ta ’yan sandan ga lauyan gwamnati Mista Abichai Mandelblit.
Ya kuma rage gare shi ya yanke hukunci game da gurfanar da Firayi Minista Netayanhu ko kuma ya yi watsi da bukatar baki daya.