’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta.
Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Janairu, 2025 ne Hukumar Babban Birnin Tarayya ta haramta ayyukan ’yan bola-jari a cikin faɗin birnin.
Umarnin ya taƙaita ayyukansu ga kan juji da ke ya yankunan da suke wajen birnin.
A lokacin zaman ne aka dakatar da ayyukan ’yan gwangwan na tsawon makonni biyu, saboda zargin alaƙarsu da ’yan bola-jari.
- NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
- Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja
An iya tuna cewa wannan lamari ya samo asali ne daga sace-sace kusan ɗauƙacin ƙarafunan murafen ramukan da ke kan titunan biran, waɗanda ake zargin ’yan bola-jari ne ke yi.
A yayin bincike da samame da aka kai a kasuwannin a sassan Abuja, jami’an tsaro sun gano ƙarafunan da wasu kayan gwamnati kamar fitilun kan titi da manyan wayoyin lantarki da sauransu a wurin wasu ’yan gwangwan.