‘Yan Najeriya sun yi tir da sabon karin farashin man fetur zuwa N143.80 da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta nuna yanzu za a rika sayar da litar man ne a kan sabon farashin, sabanin Naira 123.50 da aka saba sayarwa a baya.
- An kara farashin man fetur zuwa N143.80
- Farashin man fetur ya karye
- An sake rage farashin man fetur a Najeriya
Karin dai na zuwa ne a ranar da aka dage dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi a fadin Najeriya.
Sanarwar Hukumar da ke ke kula da Kayyade Farashin Albarkatun Mai ta Kasa (PPPRA), ta ce karin ya zama wajibi la’akari da kudaden da ‘yan kasuwa ke kashewa wajen dakon man da kuma isar da shi zuwa jihohi.
Rahotanni dai sun nuna cewa zuwa ranar Laraba, farashin danyen mai ya kan kai Dala 39.81 a kan kowace ganga.
‘Yan Najeriya da dama dai sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan matakin gwamnatin na kara farashin.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana rashin jin dadinta kan karin, tana mai kiran shi sabon salon takurawa ‘yan kasar.
Karin abin Allah-wadai ne —Kungiyar Kwadago
A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust ta waya, shugaban NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ya ce bai kamata ‘yan kasa su dandani kudar rashin yin cikakken tsari da gwamnatoci suka yi ba.
“Matukar ana son kawo karshen tashin gwauron zabin farashin mai, to dole Najeriya ta dawo tace danyen manta da kanta.
“Mun fada kuma ba za mu fasa fada ba cewa, a daidai lokacin da ya kamata gwamnati ta rage wa jama’a matsin da suke ciki sai ga shi abun takaici ta bige da kara jefa su cikin matsi.
“Wannan abin takaici ne matuka”, inji Wabba.
‘An yi karin a lokacin da bai dace ba’
Kazalika, kungiyar masu kamfanonin sufuri ta kasa (PTONA) ta nuna rashin jin dadinta da karin farashin.
Babban Sakataren Kungiyar, Ebere Oluoha ya ce, “Karin farashin mai a irin wannan yanayin sam bai kamata ba.
“Lamarin zai iya sa direbobi su kara kudin mota musamman yanzu da aka dage dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi.
Ya lura cewa hakan zai yi tasiri matuka wajen ta’azzara halin matsin da mutane suke ciki.
Ya kuma ce dama tuni kudaden sufurin suka yi tashin gwauron zabi sakamakon dokar bayar da tazara a cikin ababen hawan da ake yi a yanzu haka.
‘Kamata ya yi gwamnati ta tausaya wa al’umma’
A nasu tokacin kuwa, kungiyoyi masu zaman kansu sun ce kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da irin mawuyacin halin da yan kasa su ke ciki musamman dub da yadda annobar coronavirus ta shafi kusan dukkan harkokin tattalin arziki.
Kakakin wata gidauniya mai suna CLEEN Foundation, Benson Olugbuo ya ce, “Kamata ya yi gwamnati ta yi wa jama’a bayani karara idan karin yana da alaka da cire tallafin mai ta yadda za mu fahimta.
“Wannan karin na ba zato ba tsammani, zai yi matukar illa ga tattalin arzikin da dama yake cikin mashashshara”, inji shi Benson Olugbuo.