Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya musanta labarin karin kudin man fetur zuwa N212.11 a kan kowacce lita.
Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Kayyade Farashin Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (PPPRA) ta yi harsashen cewa akwai yuwuwar farashin man ya kai wannan adadin.
- ’Yan bindiga sun sace daliban kwaleji a Kaduna
- NAFDAC ta yi gargadi kan bullar rigakafin COVID-19 na bogi
Sai dai NNPC a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter ranar Juma’a ya kore batun karin.
PPPRA dai ta ce ta yi harsashen ne la’akari da yanayin kudaden da ake kashewa wajen shigo da albarkatun man zuwa Najeriya.
Sai dai hukumar ta ce ba lallai ne hakan ya jawo karin farashin man ba, saboda babu wata sanarwa a kan hakan har yanzu a hukumance.
A watannin Janairu da Fabrairun bana ma dai sai da hukumar ta fitar da wadannan alkaluman harsashen amma farashin bai canza ba.
Ko a kwanakin baya dai sai da Kamfanin na NNPC ya ce babu batun karin kudin man a wannan watan na Maris.