✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya miliyan 133 na fama da talauci —Rahoto

Jihar Ondo ce mafi karancin talauci a Najeriya.

Rahoton da Gwamnatin Tarayya ta fitar ya bayyana cewa, ’yan Najeriya miliyan 133 wato kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar ke fama da talauci.

Alkaluman binciken ma’aunin talauci a Najeriya (MPI) ne suka tabbatar da hakan a wannan Alhamis din a Abuja.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da Hukumar Tsara Bayar da Tallafi ga Masu Karamin Karfi (NASSCO)da Shirin Samar da Ci Gaba na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da Asusun Ilimin Kanana Yara na Unicef (UNICEF) da Shirin Yaki da Talauci da Ci Gaban Al’umma na Oxford (OPHI) ne suka gudanar da aikin kididdigar.

Binciken ya nuna cewa an karbi bayanan magidanta dubu 56 a sassan jihohin kasar 36 da Birnin Tarayya Abuja, da aka gudanar tsakanin watan Nuwamban 2021 zuwa Fabarairun 2022.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matalauta a kasar na rayuwa ne a Arewacin Najeriya, yayin da kashi 35 cikin 100, kusan mutum miliyan 47 ke nan na zama ne a Kudanci.

Sakkwato ce jihar da ta fi fama da talauci a kasar, inda kashi 91 cikin 100 na al’ummarta ke rayuwa hannu-baka hannu-kwarya, yayin da Jihar Ondo ce kuma mafi karancin talauci a Najeriya da kashi 27 cikin 100.

A lokacin da ya yi tsokaci kan alkaluman, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wannan bayani zai bijiro da hanyoyin da za a bi wajen yaki da talauci.