✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka cuci ’yan Najeriya masu neman aiki a Birtaniya —IOM

’Yan Najeriya 260,000 sun nemi yin hijira su bar kasar, a cewar Hukumar ’yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya

’Yan Najeriya 260,000 sun nemi yin hijira su bar kasar, a cewar Hukumar ’yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM).

Shugaban Ofishin IOM, Laurent De Boeck, ya ce ’yan Najeriyan sun tuntube ne ta hukumar kan yadda yadda za su yi hijira daga kasar.

Ya ce ’yan mutanen da ke naman ficewa daga Arewa maso Gabas su bar Najeriya, sun karu da kashi 30 cikin 100 a shekaru biar da suka gabaa.

A cewarsa, yawan ’yan Najeriya da aka damfara da sunan sama musu aiki a kasar Birtaniya sun haura 1,000.

Laurent ya ce wasu ’yan Najeriyan da haka ya rusa da su, sun kare a halin kakka-ni-ka-yi, ba su da kudin dawowa gida daga Birtaniya.

Wasu kuma suna jin kunyar dawowa gida Najeriya bayan abin da ya same su a kokarin su na samun aiki ta kowace hanya.

“Wasunsu sun biya sama da $10,000, amma sai a ba su takardar daukar aiki ta bogi, wadda da ita suke amfani su samu bizar zuwa Biraniya.

“Bayan sun isa, idan suka kai wa kamfanin takardar daukar aikin, sai su ji cewa ba daga kamfanin takardar daukar aikin ta fito ba.

“Mutanen da irin haka ta faru da su sun fi 1,0000,” in ji Laurent De Boeck.

Ya ce a halin yanzu hukumar na kokarin kwaso yan Najeriya da yan wasu kasashe da suka makale kasar unisia, wadda ta sa tankunkumi kan an gudun hijira.