A ‘yan shekarun baya mun zayyana yadda azumi ke da amfani ga lafiyarmu. A bana kuma za mu duba irin ‘yan matsalolin da mai azumi zai iya fuskanta da yadda zai kiyaye su. Dole ne a lokuta da dama mai azumi ya fuskanci yunwa da kishin ruwa, amma da yake manufar azumi ba ita ce galabaitar mutum ba, dole a dauki matakan rage wahalar da za ta zarta su yunwa da kishin ruwan din a yayin azumi. Wadannan ‘yan matsaloli kuwa sun hada da:
Ciwon kai da Gajiya: Duk da cewa a bana ma azumi ya zo a lokacin damina, lokaci mai ni’ima, za a iya samun zafin rana sosai a wadansu ranaku. Idan mai azumi ya fiya shiga rana, dan ruwan jikinsa zai iya saurin karewa nan-da-nan, ya sa masa ciwon kai. Idan mai azumi mai aikin karfi ne, zai iya karar da dan kuzarin da ya rage a jikinsa nan-da-nan, ya yi saurin jin yunwa da kishi da ciwon kai. Duka wadannan za a iya kiyaye su idan aka rage yawan awoyi da ake ana aikin karfi a rana. A kasashe na Larabawa misali, sukan yi aiki da safe su koma gida da rana, sai rana ta yi sanyi, ko ma an sha ruwa an yi sallah, sa’annan suke komawa harkokinsu na yau-da-kullum. Muma masu aikin karfi a cikinmu dole su rage yawan awonnin aikin rana a wannan wata, kuma mutum ya rika rike lema idan zai shiga rana, sa’annan idan an dawo gida a dan watsa ruwan sanyi a jiki kwakwalwa ta huce.
kwarnafi: Wasu a cikinmu da dama idan suka yi suhur da an yi sallah kuma sai a bi gado. Wannan na daya daga cikin manyan abin da kan kawo kwarnafi, mutum na cin abinci ba da dadewa ba sai ya kwanta barci. To da an tashi da safe sai a ji abincin nan na dawowa ko a rika gyatsarsa. Idan irinsu kwai ne ma gyatsar takan yi wari. Wannan duk sanadiyar abinci bai bi uwar hanji ba ne aka kwanta. Idan aka ci sahur, aka jira kamar a kalla awa biyu zuwa uku kafin a kwanta, lokacin ana kyautata zaton abinci ya gangara uwar hanji, za a iya kwanciya. Wato dai jinkirin kwanciya zai kiyaye aukuwar kwarnafi
kunar Zuci: Ita kuma yawanci a mutanen da ba sa suhur, ko masu ciwon olsa aka fi gani. Masana suna ganin kuma a wasu lokuta yawan tunanin abinci ma zai iya sa kunar zuci, tunda tunanin abinci na iya sa sinadarin acid ya taru a ciki ya rika kartar cikin. Yadda za a kiyaye wannan ke nan shi ne yin suhur daidai gwargwado, da yawan karatu da lazimi yayin azumin kada a rika yawan tunanin abinci. Kai ko barci ma mutum ya yi wannan ba ta faruwa saboda barcin mai azumi ma ibada ce inji malamai.
Cushewar Ciki: Banda kwarnafi da zafin ciki, akan samu wasu da sun dan bude-baki ko da ba su ci da yawa ba, cikin ya cushe, musamman ma a goman farko kafin ciki ya saba da canjin karin kumallo. Wannan ce ta kan sa a addinance (azumin nafila) da ma a kimiyyance (intermittent fasting), ake so mutum ya rika yin azumi jefi-jefi, domin yakan sa ciki ya saba, ba ma da yunwa kawai ba, a’a har da juyin lokutan karin kumallo. Za kuma a iya kiyaye hakan idan aka fara buda-baki da abin da aka saba karin kumallo da shi a ranakun da ba na azumi ba.
Matsalolin Rashin Lafiya: Masu cutukan da kan dade a jiki kamar su ciwon suga, hawan jini, olsa, asma, sikila da ire-irensu suma a lokuta da dama wasunsu sukan sha wahalar azumi. To kowane daya daga cikinsu yana bukatar shawara da likitansa a wannan shekara kafin ya dauki azumi, domin matsalar ta wani ya fi ta wani, kuma ta bana watakil ba ta kai karfin ta bara ba, ko a samu ta bana ta fi ta bara tsanani. Don haka ne ba za a yanke cewa ga wanda zai yi azumi ba, ga wanda ba zai ba, sai dai likitan da mutum ke gani ne zai iya yanke wannan shawara.
Taurin Bayan-gida: A lokuta da dama wasu sukan samu taurin bayan gida a wannan wata na Ramadana. Da ma can akan samu raguwar bayan-gidan saboda yawan cin abinci ya ragu, to amma idan ba a samun isassun ganyaye, kayan marmari da ruwa ko abu mai ruwa-ruwa lokacin bude-baki ko abincin asuba, bayan-gida zai yi gardama. Don haka yawan shan kayan marmari lokacin bude-baki da shan ruwa kamar kofi biyu gabannin alfijir zai taimaka wajen rage aukuwar wannan matsala
Gudawa: Da yake akan yawaita cin kayan ganye da na marmari, wadanda ba dafa su ake ba kafin a ci, da ruwan kankarar da yawanci ba a san daga inda ta fito ba, dole sai mai shan ruwa ya yi taka-tsantsan don kada gudawa ta bata sha’ani. Ruwa dole a samu mai tsabta, idan ba a san inda aka samo kankara ba yana da kyau a saka ta cikin ruwan da aka riga aka kulle a leda don kada ta gurbata ruwa. Sai kuma wanke kayan ganye da ruwan gishiri, wanda zai wanke duk wata kwayar cuta a jikin ganyen.
kiba: Wasu za su yi mamakin saka wannan a cikin matsalolin da mutum zai iya samu a wannan wata. Maimakon mutum ya saisaita nauyin jikinsa, sai ma ya ga yana karawa. Wannan na faruwa ne idan mutum ya dauki watan azumi a matsayin watan cika-ciki. Idan wasu suka sha ruwa suka fara ci, haka za su yi ta yi da kadan-kadan ba sa bari sai an yi assalatu, wato ba za ma su iya kirga sau nawa suka ci abinci a daren ba. Kuma ana ci da an yi sallah fa sai barci. To idan mutum ba ya so ya kara nauyi a wannan wata da ake samun wadatar abinci da kayan sha, dole sai ya yi taka tsan-tsan, kuma ya rika ci saisa-saisa, wato sau biyu kawai maimakon yadda ake ci sauran watanni. Kuma kada a cika ciki him, kada kuma a rika dauki dai-dai na tsawon daren. Kada kuma a rika saurin kwanciya bayan an ci abinci. Wadannan su ne za su sa mutum ya saisaita nauyin jikinsa, kuma da yawan mutane masu kiba ma sukan ragu a wannan wata.