✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Mali na murnar fatattakar jakadan Faransa daga kasarsu

Lamarin dai na tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Dubban masu zanga-zanga ne suka fantsama a kan titunan Bamako, babban birnin kasar Mali, don nuna kin jinin Faransa tare da murnan korar jakadanta da aka yi daga Malin a makon da ya gabata.

Yayin zanga-zangar dai, mutane sun rika daga tutocin kasar Rasha tare da kona hotunan Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, lamarin da yake nuna zaman doya da manjan da ake yi tsakanin Malin da kasar da ta yi mata mulkin mallaka.

A cewar wani jami’i a gwamnatin rikon kwaryar kasar, Moulaye Keita, “Akwai dubban ’yan Mali a yau da suke nuna kin jinin Faransa. Saboda haka, abin da ya kamata kasar da ma Tarayyar Turai su yi shi ne su girmama ra’ayin hukumomin Mali.

“Ya kamata su fahimci cewa gwamnati mai ci a yanzu, ita kadai ce za ta iya magana da yawun ’yan kasar,” inji Moulaye.

Dangantaka tsakanin Faransa da Mali dai ta yi tsami ne bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a shekarar 2020, sun janye alkawarin da suka yi tun da farko na shirya zabe a watan Fabrairu, tare da ci gaba da rike mulki har nan da 2025.

Lamarin ya dada tabarbarewa ne a makon da ya gabata, lokacin da gwamnatin Malin ta ba jakadan na Faransa sa’o’i 72 ya fice daga cikinta.

To sai dai wani tsohon mamba a gwamnatin rikon kwaryar kasar da aka sauke, Adama Ben Diarra, ya ce daukar matakin ya kankaro martabar kasar, inda ya bayyana korar jakadan a matsayin muhimmin mataki wajen dakile tasirin Faransa a Mali.

A kan batun jibge dakarun Rasha a Mali kuwa, Adama ya ce, “Saboda tabbatar da tsaron mutanen mu, ko Shaidan ne zan iya aiki da shi muddin zai taimaka min wajen fatattakar Faransa da abokanta ’yan ta’adda.”

Kasar ta Mali dai na ci gaba da kokarin ganin ta yaki ’yan tawayen da suka dauki makamai kuma suke yakarta tun shekarar 2012.