✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan Majalisar Jihar Ogun sun dakatar da sabbin Sarakunan Jihar

‘Yan majalisar jihar Ogun sun yi wata doka da zata dakatar da daukacin sabbin sarakunan gargajiya da wadanda gwamnan da ya shuxe ya yi wa…

‘Yan majalisar jihar Ogun sun yi wata doka da zata dakatar da daukacin sabbin sarakunan gargajiya da wadanda gwamnan da ya shuxe ya yi wa sarautar su karin girma tun daga watan Fabrairun shekarar nan zuwa ranar 29 ga watan Mayu wato ranar da aka rantsar da Sabon gwamnan jihar Prince Dapo Abiodun.

Haka zalika sun kuma dakatar da shugabannin sabbin kananan hukumomin da tsohon gwamnan jihar Sanata Ibikunle Amusu ya kirkira ( LCDA) domin asami damar bincikar su biyo bayan zargin su da ake da yin tabargaza da dukiyar gwamnati inda ‘yan majalisar suka bukaci da su hallara a zauren ta a ranar 7 ga watan Yuni.