Hakika muna jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane da namijin kokarinsa wajen ganin an tallafa wa matasa marasa ayyukan yi, amma kuma sai dai kuma kash! rijiya ta ba da ruwa, guga ta hana, dalilin da ya sa na ce haka kuwa, shi ne, ganin yadda ’yan majalisu suka yi watsi da kudurin bai wa talakawa marasa karfi tallafin Naira dubu biyar a kowanne karshen wata. Hakika hakan ya nuna mana cewa yan majalisun mu na Najeriya ba su kaunar talakawa afili. Don haka mu talakawan Najeriya, muna nan muna zuba ido su fito su yi mana bayanin dalilin da ya sa suka yi watsi da wannan batu na tallafa wa masu karamin karfi.
Daga Mohammed mai kaset, karamar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. 08138775015 [email protected]