Majalisar Wakilai ta amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan gabatar da rahoton kwamitin da aka kafa domin tantance shi a ranar Laraba.
- Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane
- An daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
Shugaban kwamitin da ya tantance shi, Babajimi Benson, wanda ya gabatar da rahoton, ya ce an yi wa Oluyede tambayoyi kan batutuwan tsaro na ƙasa kuma ya amsa su yadda ya kamata.
Ya ce kwamitin ya gamsu da ƙwarewarsa kuma saboda haka zai iya riƙe ofishin da aka ba shi.
Ana iya tuna cewa, a ranar 30 ga watan Oktoba ne Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Oluyede a matsayin muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa a sakamakon rashin lafiyar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Amma daga bisani, Janar Lagbaja ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024.