✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan majalisa 7 sun fice daga APC a Edo

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Frank Okiye, tare da wasu ’yan majalisa shida sun fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP, a ranar Talata. Da yake karanta…

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Frank Okiye, tare da wasu yan majalisa shida sun fice daga jamiyyar APC zuwa PDP, a ranar Talata.

Da yake karanta wasikar sauyin shekar a zauren majalisar, Okiye ya ce rabuwar kawi a jam’iyyar APC ta sa suka koma PDP don samun damar gudanar da aikinsu na wakiltar mutanensu yadda ya kamata.

Ya kara da cewa sun koma PDP mai mulki ne domin su ci gaba da tafiya yadda suka saba da Gwamna Godwin Obaseki

’Yan majalisar da suka sauya shekar su ne Roland Asoro, Ephraim Aluebhosele, Sunday Ojiezele, Henry Okhuarobor, Emma Okoduwa da kuma Marcus Onobun.

Sai dai kuma sauran ’yan majalisar uku: Emmanuel Agbaje, Yekini Idiaye da kuma Nosa Okunbor, sun ki sauya sheka daga APC.

Har wa yau a zaman, ’yan majalisar sun amince da kalandar tafiyar da ayyukan zango na biyu na majalisar.

Da ya ke gabatar da rahoton kalandar ga ’yan majalisar, Shugaban Masu Rinjaye, Henry Okhuarobor, ya ce kalandar za ta ba majalisar damar yin zama 62 a zangon na biyu.