Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya ce Kamfanin gine-gine na Julius Berger da ke kwangilar babban titin Kano zuwa Abuja, na neman naira tiriliyan 1.35 domin kammala aikin.
Da yake magana a wani taro ranar Alhamis tare da daraktocin ma’aikatar ayyukan a Abuja, babban birnin Najeriya, ministan ya ce titin da farko an ware naira biliyan 165 wanda aka ƙara kuɗin zuwa naira biliyan 654.
- Kotun Koli ta hana madugun adawar Senegal Ousmane Sonko tsayawa takara
- Har yanzu gas din girki na gagarar talaka bayan wata daya da alkawarin gwamnati
Sai dai ya ce a yanzu kuwa gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.
Ana iya tuna cewa, tun a shekarar 2017 ce Gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar amma sai a 2018 aka soma aikin.
Ya kamata a kammala titin cikin shekarar 2021 wanda ɗaya ne daga cikin ayyukan gwamnatin Buhari.
Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a 2023, inda a yanzu dai an kammala fiye da rabin aikin titin.
Ya kara da cewa ma’aikatar tana kuma nazari kan shimfiɗa titin kilomita 40 na farko da rukunin Kamfanin Dangote zai gina a karkashin Shirin Bayar da Haraji.
Ya ce galibin wurin da aikin ya rage yana buƙatar a yi masa zubin kankare saboda wuri ne da ya kasance kwarmi mai tara ruwa.
Ya kuma bayyana cewa “duk rintsi za mu kammala aikin a bana.”