✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Super Falcons sun yi garkuwa da kofin Afirka da suka lashe

Rahotannin da ke fitowa sun nuna a ranar Talatar da ta wuce ne ’yan kwallon kafa na matan Najeriya Super Falkcons suka yi garkuwa da…

Rahotannin da ke fitowa sun nuna a ranar Talatar da ta wuce ne ’yan kwallon kafa na matan Najeriya Super Falkcons suka yi garkuwa da kofin Afirka na mata da suka lashe a Kamaru.

Kofin, wanda shi ne karo na 10 da kungiyar ke lashewa, ’yan kwallon sun ki yarda su mika shi ga Hukumar kwallon kafa (NFF) ne a ranar Litinin da ta gabata a yunkurin nuna bacin ransu ga hukumar na kin biyansu hakkokinsu.
Haka kuma ’yan kwallon sun kekasa-kasa sun ce ba za su karbi Naira dubu 50 da hukumar ta ba su a matsayin kudin sallama ba, kamar yadda suka ki amincewa su bar Otel din Agura da Hukumar ta sauke su a Abuja ba.
“Mun yanke shawarar yin garkuwa da kofin Afirka na mata da muka lashe a Kamaru ne har sai Hukumar NFF ta biya albashi da alawus-alawus da muke bin ta bashi”, inji ’yan wasan a wata hira da manema labarai suka yi da su.
Su dai ’yan matan sun harzuka ne a lokacin da Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) Mista Amaju Pinnick ya kai musu ziyara a Otel din da aka sauke su na Agura da ke Abuja inda ya nuna musu ba kudin da za a sallame su. Hukumar ta yi musu tayin ba kowannensu Naira dubu 50 a matsayin kudin mota da niyyar biyansu su sauran hakkokin nasu a nan gaba idan an samu kudi. Hakan bai yi wa ’yan kwallon da jami’ansu dadi ba, inda suka ce atafau ba za su mika kofin Afirka na mata da suka lashe a Kamaru ga Hukumar ba.
Nan take shugaban hukumar ya shiga taro da ’yan kwallon da jami’ansu, amma ganin alkawari ne kawai ya yi musu a fatar baki kuma ya kasa fada musu takamaiman ranar da za a biya su hakkokin nasu ta sa aka tashi taron ba tare da an cimma matsaya ba.
Haka kuma umarnin da hukumar ta ba ’yan kwallon na barin Otel din da aka sauke su don komawa gidajensu, shi ma ya ci tura, inda suka nuna ba za su bar otel din ba har sai an biya su hakkokinsu.
Har lokacin hada wannan rahoto ba a cimma matsaya a tsakanin Hukumar NFF da ’yan kwallon da kuma jami’ansu ba don haka ba mu samu labarin ko sun bar Otel din ko a’a ba.
Idan za a tuna a ranar Lahadin da ta wuce ne kungiyar Super Falcons ta lashe kofin Afirka na mata a karo na 10 bayan ta lallasa Kamaru da ci 1-0. Sai dai tun bayan da ’yan matan suka iso Najeriya daga Kamaru gwamnatin tarayya ba ta karramasu ba, hasalima sun shigo kasar nan dauke da dimbin basussukan da suke bin Hukumar NFF bashi.