✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Super Eagles 5 masu sha’awar auren turawa

Da yawa daga cikin ’yan kwallon Super Eagles musamman wadanda ke buga kwallo a kasashen Turai sun gwammace su auri turawa maimakon matan da ke…

Da yawa daga cikin ’yan kwallon Super Eagles musamman wadanda ke buga kwallo a kasashen Turai sun gwammace su auri turawa maimakon matan da ke Najeriya ko Afirka saboda wasu dalilai na kashin kansu.  A hakan haka ne wata kafar watsa labarai a yanar gizo naij.com ta yi bincike a kan ’yan kwallo 5 na Super Eagles da suka gwammace su auri turawa maimakon matanmu na gida, ga sunayensu nan kamar haka:

 

1.  John Mikel Obi:  Cikakken sunansa shi ne John Micheal Nchekwube Obiana da aka fi kira da Mikel John Obi.  Yanzu haka yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles, hasalima shi ne kyaftin din kungiyar. An haife shi ne ranar 22 ga watan Afrilun 1987 inda yanzu haka yake da shekara 30 kuma a garin Jos aka haife shi.  Yanzu haka yana buga kwallo ne a wani kulob da ake kira Tianjin TEDA da ke kasar Sin.  Ya taba buga wa kulob din Chelsea na Ingila kafin ya canza sheka zuwa Chaina a karshen kakar wasan da ta wuce.

Sai dai dan kwallon ya gwammace ya auri budurwarsa da yanzu haka ta haifar masa ’ya’ya biyu kafin a daura musu aure mai suna Olga Diyanchenko ’yar asalin Rasha maimakon ya auri ’yar Najeriya kamar yadda yake yawan sanya hotonsa tare da budurwar tasa a shafin sadarwarsa na Twitter.  

2. William Troost Ekong:  Shi ma dan kwallon kungiyar Super Eagles ne da yanzu haka yake bugawa kulob din Bursaspor na Turkiyya kwallo.  Yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka taimaki kungiyar zuwa gasar cin kofin duniya a bana.  An haife shi ne a kasar Holand amma asalin iyayensa ’yan Najeriya ne.  Yanzu haka yana da shekaru 24. Rahotanni sun ce dan kwallon ba ya da sha’awar ya auri ’yar Najeriya, shi ma ya gwammace ya auri baturiya ce inda yanzu haka yake soyayya da wata budurwa ’yar kasar Holand kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

3. Ola Aina: Cikakken sunansa shi ne Temitayo Olufisayo Olaoluwa Aina, inda a takaice ake kiransa da Ola Aina.  Yanzu haka yana buga wa kulob din Hull City na Ingila wasa ne amma asalin kulob dinsa shi ne Chelsea.  Kulob din Chelsea ya bayar da shi aro ne ga Hull City inda akwai yiwuwar ya sake komawa can idan ya kammala kwantaragi a kulob din Hull City.  dan kwallo ne da ke buga wasa a bangaren dama a baya (right back).Shi ma a Landan aka haife shi amma asalinsa dan Najeriya ne.  Yanzu haka yana da shekara 21 kuma rahoto ya nuna dan kwallon yana da sha’awar auren Baturiya ce, ba ’yar Najeriya ba. Yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka taimaki kungiyar hayewa gasar cin kofin duniya a Rasha a wasannin share fage da aka kammala kwanan nan.

4. Carl Ikeme: Ikeme dai haifaffen Ingila ne amma asalin iyayensa ’yan Najeriya ne.  Yanzu haka gola ne a kulob din Wolberhampton na Ingila kamar yadda yake gola a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.  Shi ma an tabbatar matarsa ’yar asalin Ingila ce da hakan ya nuna ba shi da sha’awar auren ’yar Najeriya.  Rahotanni sun nuna yanzu haka sun haifi yara biyu tare da matarsa Baturiyar Ingila. Yanzu haka yana da shekara 31.

5. Brian Idowu: Brian Idowu dai yanzu haka yana buga kwallo ne a wani kulob da ake kira Ankar Perm da ke kasar Rasha.  Hasalima ya fara buga wa kungiyar Super Eagles wasa ne a ranar da aka yi wasan sada zumunta da Ajantina a ’yan kwanakin baya  inda ya samu nasarar zura daya daga cikin kwallaye hudun da Najeriya ta zura a ragar Ajantina inda aka tashi wasa 4-2. Magoya bayan kungiyar Super Eagles sun yaba da kwazon dan kwallon a ranar da da ya fara buga wa kungiyar kwallo, wato a wasan sada zumunta da kasar Ajantina a Rasha.  Yana buga kwallo ne a bangaren baya (defender) sai dai rahotanni sun nuna budurwarsa ’yar asalin Rasha ce mai suna Katerina Zagoruiko da hakan ya nuna da wuya ya auri ’yar Najeriya.  Shi ma haifaffen Saint Petersburg na Rasha ne amma asalin iyayensa ’yan Najeriya ne.