✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yan kwallon Remo Stars 10 da aka kwantar a asibiti sun samu lafiya

Aranatar Talatar da ta wuce ne aka bayar da labarin sallamar wadansu ’yan kwallo 10 na kulob din Remo Stars da ke Akure da aka…

Aranatar Talatar da ta wuce ne aka bayar da labarin sallamar wadansu ’yan kwallo 10 na kulob din Remo Stars da ke Akure da aka kwantar a asibitin Ikeme General Hospital bayan sun ci tuwon semobita da miyar ganye.


Kamar yadda labarin ya nuna, su dai daukacin ’yan kwallon  kulob din sun ci tuwon semobita ne da miyar ganye ana gobe za su hadu da kulob din Ifeanyi Ubah  a gasar rukuni-rukuni ta Najeriya mako na 28 amma jim kadan bayan sun kwanta barci sai aka ji kururuwar ’yan qwallon suna neman a kai musu dauki saboda tsananin ciwon da cikinsu yake yi.

Likitan kulob din ya ce ya kaxu matuqa bayan an sanar da shi halin da ’yan qwallon suka shiga kuma nan take ya bayar da umarnin a garzaya da su asibiti don a yi musu magani.
Wannan al’amari ya faru ne a ranar Asabar da ta wuce da hakan ta sa aka daga wasan da kulob din Remo din zai yi da na Ifeanyi Ubah har zuwa wani lokaci saboda matsalar da ’yan qwallon suka fuskanta.


“Duk da irin matakin da muka dauka a sansanin horar da ’yan qwallon na yin feshin da ke kashe sauro da na wadansu qananan qwari amma sai ga shi ’yan qwallon sun kamu da rashin lafiya bayan sun ci abinci”, inji Likitan kulob din Remo Stars. ’Yan qwallon da suka kamu da wannan cuta sun haxa da Ekene Awazie da Victor Mbaoma da Abiodun Awoyemi da Umar Martaba da Okamogabre Osas da Edozie Ewelike ada kuma Onovo David.
Sauran sun hada da Ekene Obi da Sa’idu Muhammed da kuma Paul Isaac.