✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Najeriya 3 da ke daukar sama da miliyan 30 a sati

’Yan wasan kwallon kafa na daukar makudan kudade a duk sati a matsayin albashi.

Kwallon kafa wasa ne da ya yi fice a fadin duniya kuma daga cikin ’yan wasansa akwai masu daukar makudan kudade a matsayin albashinsu a duk mako.

A Najeriya akwai wasu shahararrun ’yan wasa kwallon kafa da ke daukar fiye da Naira miliyan 30 a matsayin albashinsu, a duk mako.

1. Victor Osimhen:

Osimhen dan wasan gaban Najeriya ne da ke murza leda a kungiyar Napoli da ke kasar Italiya, inda yake daukar £120,000, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 67 a matsayin albashinsa a sati.

2. Kelechi Iheanacho:

Iheanacho na taka rawar gani a bana a kungiyarsa ta Leceister City da ke kasar Birtaniya.

Dan wasan yana daukar albashin £60,000 a duk sati, wato kimanin Naira miliyan 33.

3. Wilfred Ndidi:

Ndidi dan wasan tsakiya ne dan asalin Najeriya da ke taka leda a Leceister City a gasar Ingila.

Dan wasan ya yi fice, wanda ya sa kungiyarsa ke biyan shi £76,000, kimanin Naira miliyan 43 a duk mako.

Wadannan makudan kudade da ’yan kwallo ke dauka duk sati, ya sa mutane da dama ke tururuwar neman kungiyar da za ta dauke su musamman a kasashen Turai.