✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwallon Lobi Stars sun tsallake rijiya da baya

“Yan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta Lobi Stars sun tsallake rijiya da baya a daren Litinin yayin da motarsu ta kama da wuta a hanyarsu…

“Yan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta Lobi Stars sun tsallake rijiya da baya a daren Litinin yayin da motarsu ta kama da wuta a hanyarsu ta dawowa gida daga Ilorin ta  Jihar Kwara inda suka fafata wasan mako na 22 na gasar Firimiya da Kungiyar Kwara United.

Duk da cewa ’yan wasa 10 ne suka fafata wasan da Kwara United, Lobi Stars ta yi nasara a kan Kwara United da ci daya mai ban haushi. Kuma a hanyarsu ta komawa Makurdi ne wannan hadari ya faru a garin Adaka da ba ya da nisa  da Makurdi babban birnin Jihar Binuwai.

Sanarwar da Kakakin Kungiyar, Austine Tyowua, ya fitar ta ce wannan lamari ya faru ne sanadiyyar tangardar wayoyin wuta da motar ta samu, lamarin da ya sa motar ta kama da wuta, kuma duk kokarin da suka yi don kashe wutar ya ci tura.

“Duk da yake ba a rasa rai ba a cikin hadari, amma an yi asarar kaya da muhimman takardu, musamman na motar domin babu abin da aka fitar daga cikinta,” inji shi.

Sanarwar ta ce, ’yan wasan da suka samu rauni a kokarin kubuta daga cikin motar ta taga suna karbar jinya. Kuma mahukuntan kungiyar sun jajanta wa ’yan wasan tare da karfafa musu gwiwa inda suka bukaci su manta da abin da ya faru su ci gaba da maida hankalin wajen ganin sun cinye gasar.