✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kwadago sun bukaci Tinubu ya mayar da mafi karancin albashi N200,000

Kungiyar ta ce haka ne zai yi daidai da radadin cire tallafin mai

Kungiyar Kwadago ta TUC, ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya mayar da mafi karancin albashi ya koma N200,000.

Kungiyar ta ce yin hakan ne zai sa abun da ma’aikatan kasar ke samu ya yi daidai da karin farashin da ake fama da shi sakamakon cire tallafin man fetur.

Ta kuma ce ya zama wajibi a aiwatar da karin kafin karshen watan Yuni ta yadda za a iya aiwatar da tanade-tanaden Dokar Man Fetur ta Najeriya.

Shugaban kungiyar na kasa, Festus Osifo, da Sakatarenta, Nuhu Toro ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwar da suka fitar ranar Litinin.

Sun kuma ce hakan na cikin irin bukatun da suke da su kan tattaunawar da ake yi da gwamnati a kan batun cire tallafin man.

Sanarwar ta kuma ce dole ne a sami wakilcin Gwamnonin Najeriya, kuma dole ne dukkan Gwamnonin kasar nan su amince za su aiwatar da tsarin.

Sun kuma ce, “Ya kamata a kirkiro da wani alawus na man fetur ga dukkan ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da ke karbar kasa da N200,000, ko Dalar Amurka 5000, ko duk wanda ya fi yawa a tsakaninsu.

“Ya kamata kuma a samar da wani tsayayyen tsari inda duk lokacin da aka samu kari, to shi ma albashi zai karu kai tsaye, har nan da shekaru 10 masu zuwa.”