✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kungiyar IPOB sama da 200 sun yi gangami a Abakaliki

Fiye da mutum 200 da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra, suka bazama kan titunan birnin Abakaliki a jihar…

Fiye da mutum 200 da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra, suka bazama kan titunan birnin Abakaliki a jihar Ebonyi, a yau domin wata zanga-zangar lumana.

Wakilin Aminiya a birnin, ya ruwaito cewa, da akwai jami’an ‘yan sandan rundunar SARS da ke musu rakiya, yayin zanga-zangar lumanan.

Ya kuma bayar da rahoton ganin ‘yan kungiyar ta IPOB da danyen ganye a lebbansu yayin da kuma suke ta rera wake-waken ballewa.

Cikin wadanda suka shiga macin na yau, akwai tsoffi da kuma matasa na kungiyar.

Galibin su, sun rike tutocin kungiyar ta ‘yan Biafra, masu neman ballewa, rike da hannayen junansu inda suka karade manyan titunan birnin Abakaliki.

Zanga-zangar, wacce ba ta kai ga rikidewa zuwa tashin hankali ba, ya zuwa lokacin hada rahoton, ta sanya fargaba da zullumi a zukatan jama’ar birnin tare da kawo tsaikon zirga-zirgar ababen hawa dama na harkokin kasuwanci.

Wakilin namu, ya ruwaito cewar, masu zanga-zangar, sun hau kan titin Gunning, yayin da suka dangana zuwa babbar kasuwar birnin, da aka fi sani da kasuwar Abakpa, cikin birnin na Abakaliki.