✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwar ‘New market’ da ke Jos sun yi sababbin shugabanni

‘Yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar New market da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun zabi sababbin shugabanninsu. Sun…

‘Yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar New market da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun zabi sababbin shugabanninsu.
Sun gudanar da zaben ne a harabar kasuwar a makon jiya.
Sababbin shugabannin da aka zaba sun hada da Malam Isma’ila A. Garba; Shugaba da Magaji Ahmad Ayuba; Mataimakin Shugaba na I da Abdullahi Yunusa; Mataimakin Shugaba na II da Hafizu Salihu Nakande; Sakatare da Yahaya Ahmad; Mataimakin Sakatare.
Sauran shugabannin su ne Idris Ibrahim; Ma’aji da Nabil Abubakar Ahmad; Sakataren Kudi da Abubakar Shu’aibu; Sakataren Tsare-tsare da Mamuda Sa’id; Mataimakin Sakataren Tsare-tsare da Nasiru Sabi’u; Jami’in Hulda da Jama’a na I da Shehu Alhaji Bala; Jami’in Hulda da jama’a na II da Yusuf Sulaiman; Mai binciken kudi da Alhaji Sabo Inuwa; Mai bayar da shawara da kuma Alhaji Hassan Umar a matsayin  uban kungiya.
Sabon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Malam Isma’ila A. Garba ya bayyana matukar farin cikinsa sakamakon zaben su da aka yi.
Ya ce “Babu shakka mun yi matukar farin ciki sakamakon zaben mu da aka yi, musamman ganin an yi zaben a cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin ‘yan wannan kasuwa ta New market. Da yardar Allah ba za mu ba ’yan kasuwar kunya ba.”
“Za mu tsaya mu ga cewar mun kare hakkokin dukkan ’yan kasuwar. Don haka ina fata ’yan kasuwa za su ci gaba da ba mu goyan baya da hadin kai, domin mu samu damar aiwatar da kudurorin da muka sanya a gaba.” Inji shi.