✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan kasuwan Potiskum sun bukaci gwamnati ta cika musu alkawari

Shugaban kungiyar Hadakar ’Yan Kasuwan Potiskum a Jihar Yobe, Alhaji Isa Sakatare ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarin da ta dauka kafin…

Shugaban kungiyar Hadakar ’Yan Kasuwan Potiskum a Jihar Yobe, Alhaji Isa Sakatare ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarin da ta dauka kafin mutane su dawo daga rakiyarta.
Alhaji Isa Sakatare ya bayyana haka ne don nuna rashin jin dadinsa kan alkawarin da aka yi musu ba a cika ba, “An sa mambobinmu sun cika takardu da niyyar za a ba su rance, amma har yanzu shiru. Daga bara zuwa bana mun cika fom na neman rance da kuma neman tallafi fiye da iri shida daga bankunan ba da rance mai sauki ga ’yan kasuwa da kuma kungiyoyin ba da tallafi kan abin da ya shafi yankunan da suka sha fama da rikicin Boko Haram, amma har yanzu ba mu samu ko guda ba,” inji shi.
Ya ce “Don haka muke kira ga duk wanda abin ya shafa cewa, in har da gaske suke su gaggauta taimaka wa al’ummomin Arewa-maso-Gabas musamman jihohin Borno da Adamawa da Yobe domin rage radadin matsalolin da suke fuskanta.”
A karshe ya nemi ’yan kasuwan su ci gaba da ba da goyon baya ga wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari don ta kai ga nasara..