✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwan Arewa-maso-Gabas sun jajanta wa Jihar Gombe

Mataimakin Shugaban kungiyar ’yan kasuwar shiyyar Arewa-maso-Gabas kuma shugaban ’yan Kasuwar Wunti da ke Jihar Bauchi, Alhaji Arma Ya’u Yahaya ya bayyana rashin jin dadinsa…

Mataimakin Shugaban kungiyar ’yan kasuwar shiyyar Arewa-maso-Gabas kuma shugaban ’yan Kasuwar Wunti da ke Jihar Bauchi, Alhaji Arma Ya’u Yahaya ya bayyana rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ’yan kunar bakin wake suka tada wasu tagwayen bama-bamai a babbar kasuwar Gombe a ranar alhamis din makon jiya.
Shugaban ya ce hakkin gwamnati ne ta kare rayuwa ka dukiyoyin al’umma, amma ya zamo wajibi mu rika gudanar da bincike a kasuwannin mu domin kaucewa fadawa tarkon mahara.
Ya kara da cewa lokacin da muka samu labarin abin da ya faru kowa hankalinsa ya tashi. “Kuma mun yi bukukuwan sallah ne cikin bacin rai da rashin kwanciyar hankali. A yanzu haka akwai wani tawaga mai karfi da muka shirya domin kai ziyarar jaje ga gwamnatin Gombe bisa abin da ya faru,” inji shi.
Har ila yau, ya yi fatan Allah Ya ba wadanda suke kwance a asibiti lafiya shi. “Muna kuma fatan gwamnan Gombe Alhaji Ibrahim dan Kwambo zai tallafawa iyalan ‘yan kasuwar da suka rasa rayukansu,” inji shi.