A kokarinsu na tilasta dokar zaman gida a Jihar Enugu, ana zargin ’yan kungiyar awaren Biyafara ta IPOB da kashe mutum biyu ranar Litinin tare da kona wata mota kirar Sienna.
Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne a kusa da shatale-talen Chris Chemist da ke cikin birnin Enugu.
- ’Yan bindiga Sun Yi A won Gaba da Budurwa A Zariya
- An yi zanga-zangar cika shekara 3 da hambarar da gwamnatin Al-Bashir a Sudan
Aminiya ta gano cewa tsagerun sun yi ta harbe-harbe da bindiga, lamarin da ya firgita jama’a tare da sanya su gudun neman mafaka.
Da yake ba da bayani kan yadda harin ya faru, direban motar da aka kona ya ce, tsagerun sun shigo garejin da yake lodi ne cikin wata ’yar karamar mota bas kana suka tarwatsa jama’a da harbe-harben bindiga.
A cewar direban wanda aka sakaya sunansa, “Na fahimci cewa mutum biyu ne aka bindige har lahira wasu kuma sun ji rauni yayin harin da ya shafe wasu ’yan mituna, ko da na waiga baya don in ga abin da ke faruwa sai na ga motata tana ci da wuta.”
Sai dai bayanan ’yan sandan yankin sun ce mutum daya ne ya rasa ransa yayin harin sabanin mutum biyu da aka yi zargin sun mutu.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar, Daniel Ndukwe ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce jami’ansu sun soma bincike domin kamo wadanda ke da hannu cikin lamarin.