’Yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar awaren Biyafara ta IPOB ne sun kashe baturen ’yan sanda (DPO) na Karamar Hukumar Idemili ta Arewa da ke Jihar Anambra, da wasu mutum biyu.
Aminiya ta gano cewa maharan, masu tarin yawa sun yi wa ofishin ’yan sandan kawanya wajen misalin karfe 2:18 na daren Lahadi, inda suka bude wa ’yan sandan wuta.
- Buhari ya inganta Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015 – Lai Mohammed
- Masu zanga-zanga kan canjin kudi sun kona bankuna 2 a Ogun
Rahotanni sun ce ’yan sandan, tare da gudunmawar sojoji, sun mayar da martani inda suka kashe uku daga cikinsu.
Sai dai duk da haka, maharan sun kashe DPOn, da kuma wani Kwanstabul da ba a dade da tura shi yankin ba, sai kuma wani Insfekta.
Harin na zuwa ne kasa da awa 24 bayan ’yan IPOB din sun kai wani harin kan ofishin ’yan sanda na 3-3 da ke Karamar Hukumar Oyi, inda aka kashe akalla shida daga cikin maharan.
Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun rika harbi a iska lokacin da suka shiga garin, kuma an shafe tsawon sa’o’i ana jin karar harbe-harben
Kazalika, majiyar ta ce an sami nasarar kwace bindigogi kirar AK-47 guda biyu da motocin da suka kai harin da su.
Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar ta Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.