✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan fim ba su bata tarbiyya – Sadik Sani Sadik

Fitaccen jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce kwarewarsa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere. A cewarsa “Idan har…

Fitaccen jarumin Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce kwarewarsa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.

A cewarsa “Idan har ina cikin Kannywood, ni ne zan ci gaba da lashe gasar jarumin jarumai a ko wacce shekara saboda ba na wasa da aikina”, in ji Sadik Sani Sadik, a wata tattaunawa ta musamman da jarumin ya yi da BBC Hausa.

Hakanan kuma jarumin ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a fim ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali Nuhu da Adam Zango, inda ya ce “su iyayen gidana ne domin kuwa sun taimaka min sosai a wannan harkar. Ka ga kuwa babu wanda zai ja da iyayen dakinsa.”

Ya kara da cewa “Ni ina yin fim ne a matsayina na Sadik Sani Sadik, kuma ina da kwazo, da jajircewa, da mayar da hankali sosai a kan aikina, shi ya sa nake ganin babu wata gasa da za a yi da ba zan lashe ba.”

Jarumin ya ce a baya ya yi kiwon karnuka sosai shi ya sa “da aka sa ni a wani fim a matsayin mafarauci ban fuskanci wata matsala ba”.

“Abin da ya sa nake iya taka ko wacce rawa shi ne, na yi hulda da mutane daban-daban a rayuwa tun ma kafin in soma fim. Shi ya sa idan aka sa ni a matsayin mai sayar da shayi, misali, za ka ga na yi abin tamkar mai shayin gaske saboda na taba yin hulda da shi,” in ji jarumin.

Ya ce ba aikin ‘yan fim ne koyar da mutane tarbiya ba kamar yadda wasu ke hasashe, yana mai cewa, “duk wanda ya ce ‘yan fim sun bata masa tarbiyya da ma ba shi da ita. Ai tun daga gida ake samun tarbiyya