✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kashe mai gadin asibiti, sun sace janareta a Abuja

Sun dauke janaretan asibitin bayan kashe mai gadin.

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki cibiyar kiwon lafiya da ke kauyen Piri a Karamar Hukumar Kwali a yankin babban birnin tarayya, inda suka kashe mai gadi suka sace janareta kirar Mikano.

Wani mazaunin garin, Samuel Bamayi ya ce a ranar da misalin karfe 12:00 na dare lokacin da mai gadin mai suna Ishaku ya hangi ’yan fashin sai ya yi harbi a iska domin tsorata su.

“Bayan ’yan fashin sun kashe mai gadin, sai suka umarci wani direban babbar mota da suka zo da shi ya dauke janaretan asibitin,” in ji Samuel.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce za ta yi bincike domin yin karin haske.