’Yan fashi a Jihar Legas sun tare wata motar dakon kudi mallakin wani bankin zamani sannnan suka kwashe makudan kudade.
Rahotanni sun ce fashin ya faru ne a kan titin Ado da ke unguwar Ajah a Karamar Hukumar Eti-Osa da yammacin Alhamis.
Lamarin dai ya jefa tsoro a zukatan masu amfani da hanyar inda yawancinsu suka rika gudu domin tsira da rayukansu.
Fashin ya kuma firgita Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas.
Sai dai Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Hakeem Odumosu, da kakakin rundunar sun ki yarda su ce uffan game da lamarin inda suka yi ta kashe wayarsu idan an kira.
Yadda lamarin ya faru
Wasu majiyoyi sun ce ’yan fashin sun yi wa motar kofar rago ne bayan ta fito daga wani katafaren shagon sayar da kayayyaki a unguwar ta Ajah inda ta je dauko kudi, kafin daga bisani su yi nasarar fasa ta.
Majiyar ta ce sai da maharan suka bude wa mutanen da ke cikin motar wuta kafin su cim musu.
Majiyar ta kara da cewa harsashin maharan ya kuma samu wani dan acaba wanda a nan take ya ce ga garinku nan, yayin da direban motar da dan sandan da ke mata rakiya suka yi rauni.
Dukkan yunkurinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Tun fara zanga-zangar #EndSARS dai rayuwar jami’an tsaro ke fuskantar barazana a wasu sassan Najeriya, lamarin da ya sa suka yi karanci har bata-gari kan ci karensu ba babbaka.