Tsofaffin ma’aikatan gwamnati a jihar Anambra sun ce nan ba da jimawa ba za su tsunduma yajin cin abinci domin tilasta wa gwamnan jihar, Willie Obiano ya biya su kudaden sallamar su na tsawon shekaru hudu.
Shugaban kungiyar ’yan fansho na jihar, Mista Anthony Ugozor ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya ba Aminiya a Awka, babban birnin jihar ranar Litinin.
Ya ce ’yan fanshon a jihar na bin gwamnati hakkokin su na kudaden sallama da suka kai na shekaru hudun, yana mai cewa farkon sabuwar shekarar 2021 za su tattauna domin duba yuwuwar daukar matakin.
Kungiyar ta ce, “Ba mu san me za mu yi ba yanzu haka. Saboda an ga yanzu ba aiki muke yi ba, gwamnati ta san ba za mu shiga yajin aiki ba shi yasa take yi mana wannan cin kashin.
“Akwai yuwuwar mu tsunduma yajin cin abinci. Kawai abinda mu ke fargaba shine ko yunwar za ta iya yi mana illa la’akari da yawan shekarun mu, amma idan aka zo taron mu na gaba, mambobi za su yanke shawara.
“An biya ni kudin fansho na na watan Disamba tun kafin Kirsimeti, muna godiya ga gwamna akan haka, amma ba fansho kawai muke da bukata ba, muna mutuwar tsaye, ya kamata gwamnati ta biya mu kudaden sallamar mu,” inji shi.
Ya ce rabon da gwamnatin jihar ta biya wani ma’ikaci kudin salllamar sa tun shekarar 2017.
“Babu wani ma’aikacin da ya yi ritaya a shekarun 2017, 2018, 2019 da 2020 da ya karbi kudaden sallamar sa.
“Saboda haka, lamarin yana ci mana tuwa a kwarya wanda ya sa ya zama wajibi na fadawa ’yan jarida don su shaida wa duniya halin da muke ciki. Na san jami’an gwamnati ba sa murna da abinda nake yi, amma babu wanda zai rufe min baki daga faden gaskiya.
“Idan ban fadi gaskiya a shekaru na ba, tarihi ba zai taba mantawa da ni ba.
“A shekarar 2010, an kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa N18,000, amma ko sisi ba a ba ’yan fansho ba.
“A 2015 ma gwamnan ya kara wa ma’aikatan jihar albashi, 2020 kuma an kara mafi karancin albashi zuwa N30,000, amma babu wanda ya waiwaye mu. To a kan wanne dalilin zan yi shiru?” inji shi.