✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan daba sun datse al’aurar wani dan sanda

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ‘Yan daba da suka karbe zanga-zangar #EndSARS sun kashe jami’anta biyu tare da datse wa Sufeton Dan Sanda, Egu…

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ‘Yan daba da suka karbe zanga-zangar #EndSARS sun kashe jami’anta biyu tare da datse wa Sufeton Dan Sanda, Egu Omini, al’aura a Jihar Ebonyi.
Kwamishinan ‘Yan sanda jihar, Philip Maku, ya ce ‘yan daba da ya ke zargin ‘Yan Kungiyar awaren Biafra ta IPOB ne, sun sace bindigogin ‘yan sadan da suka kashe.
“An kashe mana ‘yan sanda biyu da suka hada da Sufeto Egu Omini da PC Akpu Paul.
“An kuma raunata mana ‘yan sanda 4: ASP Akili Benson, Sufeto Okewu Sunday, Sufeto Egun Omini da kuma PC Ali Samson a harin da suka kai”, kamar yadda ya sanar a ranar Alhamis.
Kwamishinan ya ce, a harin da ‘Yan dabar suka kai babban ofishin ‘Yan sanda na tsakiyar gari Inugi, ranar  26 ga wata Oktoba, 2020, sun kone ofishin da motar sintiri da kuma motocin da ke gudanar da bincike Kansu da kekuna da baburan masu laifi da sauran kayayyaki.
 
“Da farko sun yi harbe-harbe kafin su yi wa sufeto Egu Omini kisan gilla su datse masa mazakuta su sace masa bindiga kirar AK-47,” inji kwamishinan.
 
Aminiya ta ruwaito cewa ‘Yan sanda hudu da aka raunata suna samun sauki a asibiti.