Akalla ’yan ci-rani 12 da ke kokarin tsallakawa kasashen Turai ne aka tsinci gawarwakinsu bayan sun daskare a dusar kankara a kan iyakar kasashen Turkiyya da Girka.
Rahotanni sun ce ko sutturar kirki babu a jikin mutanen da aka gano.
- Benzema ba zai buga wa Real Madrid wasanta da Athletic Bilbao ba
- Najeriya A Yau: Ma’anar hijabi a idon duniya
Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya, Suleyman Soylu, ya wallafa hotunan mutanen bayan an disasar da su a shafin Twitter, shimfide a gefen hanya a kusa da garin Ipsala da ke Arewa maso Yammacin kasar, suna sanye da gajerun wanduna da rigunan T-shirt, duk da sanyin da ake fama da shi.
Ya yi zargin cewa mutum 12 na daga cikin dimbin wadanda kasar Girkar take yi wa korar kare.
“12 daga cikin ’yan ci-rani 22 da Girka ta kora sun daskare a dusar kankara sannan suka mutu, bayan an cire musu sutturarsu da takalma,” inji Ministan.
Tsananin sanyi dai a yankin ya kai kusan tsakanin digiri biyu zuwa uku a ma’aunin celcius da daddare a karshen watan Janairu da kuma farkon Fabrairu.
Minista Suleyman ya zargi masu tsaron iyakar na Girka da nuna rashin imani a kan mutanen, inda ya kuma ce Tarayyar Turai na da rauni matuka.
Ita kuwa a nata bangaren, kasar Girka, ta bakin Ministan Shige da Fice na kasar, Notis Mitarachi, ta bayyana lamarin a matsayin babbar masifa, amma ta zargi Turkiyya da siyasantar da lamarin.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) dai ta ce ita ma ta kadu matuka da jin labarin mutuwar mutanen.
Wani rahoto da Hukumar Kula na ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya kiyasta cewa sama da mutum 2,500 ne ko dai suka mutu ko kuma suka bace a kokarinsu na tsallakawa Turai daga Arewacin Afirka da Turkiyya a shekarar 2021 kawai.