✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bola sun mamaye kasuwar Sakkwato bayan gobara

Daruruwan ’yan jari bola sun mamaye kasuwar bayan gobarar awa 10

Masu sana’ar bola, da aka fi sani da jari bola sun mamaye Babbar Kasuwar Garin Sakkwato bayan gobarar ranar Talata da ta babbake kasuwar.

Washegarin ranar da aka yi gobarar ta tsawon awa 10 ne Aminiya ta ga daruruwan ’yan jari bola ne suka yi wa kasuwar tsinke da buhuna a baro suna tsintar kayayyakin da suka kone.

Wakilinmu ya gano cewa wasu daga cikin ’yan kasuwar da gobarar ta lakume kadarorinsu ne suka gayyato ’yan jari bolan domin su zo su saya su kuma cire abin da ya yi saura na daga kayansu da suka kone.

Har yanzu da ba a kai ga gano musabbabin gobarar ba a hukumance, duk da cewa wani jami’in kwana-kwana da ya bukaci a boye sunansa ya danganta gobarar da wani janareton wutar lantarki.

Wike ya ba da tallafin N500

Bayan barnar da gobarar ta kimanin awa 10 ta yi, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi alkawarin ba da tallafin Naira miliyan N500 domin taimaka wa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sake gina kasuwar.

A yayin ganawarsa da Gwamna Aminu Tambuwal, Wike ya bayyana cewa za a yi amfani da wani bangare na Naira miliyan 500 din wajen tallafa wa ’yan kasuwar gobarar ta yi wa barna.

Yayin karbar ziyarar Wike wanda ya je domin yi masa jaje kan gobarar, Gwamna Tambuwal ya ce shaguna 16,000 ne a kasuwar kuma gobarar ta cinye sama da kashi 60% na shagunan.

Shi ma da yake jajantawa, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana kaduwarsa game da irin asarar da aka tafka sakamakon gobarar.

Ya ba wa ’yan kasuwa da gwamnatin jihar hakuri game da abin da ya faru, wanda ya bukaci su dauke shi a matsayin kaddara tare da fatar Allah Ya maye musu da mafi alheri.