Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige, ya ce manyan ’yan bokon yankin Kudu maso Gabas na amfani da wani salo na yaudarar Gwamnatin Tarayya domin rura wutar neman ballewar yankin.
Ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja yayin wani taron gaggawa da kungiyar ’yan kabilar Ibo mazauna jihohin Arewa 19 da Abuja suka shirya domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan kashe-kashe marasa kan gado tare da lalata kadarorin gwamnati da ke faruwa a yankin Ibo.
Ministan ya ce: “An juya tunanin mutane inda ’yan awaren ke fakewa da hakan suna ihun cewa za mu kafa muku kasar Biyafara kuma da zarar mun kafa kasar to dukkanin wadannan ababuwan da kuke gani (na rashin adalci) za su kau.
“Babu kasar da ba ta da irin nata kalubalen. A nan muna fama da matsalolin tattalin arziki wanda shi ne silar rashin aikin yi duba da yadda muke da tarin matasa.
“Kimanin kashi 60 na al’ummarmu matasa ne kuma galibinsu zauna gari banza ne. Amma gwamnati na duba hanyoyin magance matsalar don ina da tabbacin ana aiki kan hakan.”
’Yan bindigar da ake zargin ’yan haramtacciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra ta IPOB, sun kashe jami’an tsaro tare da lalata kafofin gwamnati a yankin Kudu maso Gabas.