✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Boko Haram sun kai hari wani gari a Borno, sun yi kiran Sallah

A ranar Asabar wasu masu tayar da kayar baya cikin ayarin motoci sun kai hari kan wani kauye da ke da ’yar gajeruwar tazara tsakaninsa…

A ranar Asabar wasu masu tayar da kayar baya cikin ayarin motoci sun kai hari kan wani kauye da ke da ’yar gajeruwar tazara tsakaninsa da garin Askira Uba a jihar Borno.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa maharan da ake zargi mayakan Boko Haram ne dauke da bindigogi sun samu shiga kauye salin-alin cikin sauki da Yammacin Asabar.

Mashaidin ya ce maharan sun shiga kauyen cikin azama kuma a gadarance ba tare da sun fuskanci wata tirjiya ta jami’an tsaro ba.

Aminiya ta ruwaito cewa masu tayar kayar bayan sun yi kiran Sallah da babbar murya bayan saukarsu a kauyen inji shaidar.

Sai dai akwai rahotanni masu cin karo da juna dangane da adadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma rashin tabbas kan rahoton arcewar maharan.