Wani kwamandan Boko Haram Adamu Muhammad da wasu mayakansa biyar sun mika wuya ga sojojin a Monguno da ke Jihar Borno a ranar Alhamis.
Babban jami’in yada labaran rundunar sojin na N’djamena-Chad, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa wadanda suka mika wuya sun kawo adadin ’yan ta’addan da suka tuba tun bayan a wata daya da ya gabata zuwa 119.
- Yadda bikin mika wa Muhammadu Sanusi II takardar aiki ke gudana
- Dan Sanda Ya Kama Masu Ba Shi Cin Hancin N400,000 a Borno
A cewarsa, ’yan ta’addan sun tsere daga maboyar kungiyar ISWAP a Jubillaram, da ke Kudancin tafkin Chadi.
Ya ce, “Adamu, mai shekaru 22, ya kai hare-haren ta’addanci da dama, ya kuma yi yawo sosai a yankunan da ake fama da ta’addanci a jihar Borno.
“A lokacin da suka mika wuya, sun mika harsashi na musamman guda 11 na 7.62mm da harsashin harbo jirgin sama guda daya”
MNJTF ta yi kira ga sauran ’yan ta’adda da su yi koyi da waɗanda suka mika wuya, su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya.
Ya ce, suna jaddada aniyarsu ta tabbatar da ingantaccen wurin rayuwa a yankin tafkin Chadi.