✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘’Yan bindigar da suka kai wa maniyyatan Sakkwato hari sun kashe ’yan sanda 6’

Sai dai rundunar ’yan sanda ta ce ba ta da masaniya

Wani ganau a inda ’yan bindiga suka kai wa maniyyata hari a Jihar Sakkwato ranar Litinin ya ce maharan sun kashe ’yan Sandan kwantar da tarzoma guda shida a musayar wutar sa suka yi.

Idan dai ba a manta ba, maniyyatan sun nufi birnin Sakkwato domin tafiya sauke farali, in da ’yan bindiga suka far musu a kusa da dajin Gundumi.

Haka zalika mun kawo muku labarin yadda ’yan sandan suka mayar da maniyyatan zuwa fadar Sarkin Gobir Isa ba tare da ko kwarzane ba.

To sai dai wani mazaunin garin Isan da ya nemi a sakaya sunansa ya sanar da wakilinmu cewa ’yan Sanda shida sun mutu sakamakon harbin ’yan bindigar.

A cewar majiyar, “Yan bindigar sun yi kwanton bauna ga ayarin motocin da ke karkashin jagorancin ’yan sandan kwantar da tarzoma masu dauke da makamai.

“Jami’an da ke gaba sun budewa ‘yan bindigar wuta, abin da ma ya sa maniyatan suka samu aka juya da su zuwa Isa ke nan,” inji shi.

Rahotanni dai na nuna wannan ne dalilin da ya sanya Hukumar jin dadin Alhazaj Jihar ta canja lokacin tashinsu zuwa kasa mai tsarkin daga Talata zuwa Laraba.

A hannu guda kuma, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, ASP Ahmad Rufa’i ya ce ba a sanar da shi mutuwar jami’an ba a hukumance, amma wata majiya daga ‘yan Sandan ta tabbatar wa wakilinmu mutuwar ta su.