Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara za ta dauki ’yan asalin jihar guda 3,850 a matsayin kuratan ’yan sanda na musamman domin yaki da ’yan biniga a jihar.
Kakakin rundunar, SP Shehu Mohammed, ya ce mutum 3,850 din na daga cikin kuratan ’yan sanda na musamman 7,500 da Shugaban ’Yan Sanda na kasa, ya ba da izinin a horas domin aikin a Jihar.
- An cafke matar da ta kashe ’ya’yanta 2 a Kano
- Dalilin da na aurar da ’yata da marayu 13 – Sanata Marafa
“Nan gaba za a sanar da lokacin da za a fara horas da rukuni na gaba”, inji shi.
Ya ce an kammala tantance wadanda suka samu nasara a rukuni na farko kuma za a horas da su a makarantun horas da kananan ‘yan sanda da ke Kaduna da Sakkwato.
Rundunar ta bukaci wadanda suka nemi aikin da su duba ofisoshinta da ke kananan hukumomin jihar gabanin a fara ba su horon a ranar 9 ga Oktoba.
Sanarwar ta bukaci mutanen da suka samu nasara da su hallara a ofishin rundunar da ke Gusau a ranar 8 ga Oktoba, inda daga nan za a wuce da su zuwa cibiyoyin da za a horas da su.