✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin Ilori

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin Ilori Alhaji Usman Adamu, Hardon Hardodin Jihar Kwara.…

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin Ilori Alhaji Usman Adamu, Hardon Hardodin Jihar Kwara.

Malam Ibrahim dan jarida da ke zaune a garin  Ilori Babban birnin Jihar Kwara ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan fashin sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin da safiyar Alhamis 3 ga watan Satumba a cikin garin Ilori.

“Yana cikin mota ne tare da dansa mai suna Babangida kuma ana zaton yana kan hanyarsa ce ta zuwa banki, yana dauke da kudi zai kai banki.

“Mutanen sun tare masa hanya ne da motarsu, suka sa shi ya fito sai suka tafi da shi a cikin motarsu.

“Lamarin ya faru ne a cikin garin Ilori, da safiyar Alhamis, a daidai kofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori.

“Daga baya an gano motarsa da wayoyinsa a cikin motar, yanzu haka motar na ofishin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara”,  inji shi.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar Ajayi Okasome, amma ya yanke kiran wakilin namu.

Wakilin Aminiya ya gabatar masa da kansa, inda ya aike masa sakon  karta kwana, amma Ajayi Okasome bai  mayar da sakon karta kwanan  ba.

Uwargidan Sarkin Fulanin, Hajiya Aina’u, ta tabbatar wa Aminiya cewa an yi garkuwa da mijinta, inda ta bukaci al’umma su sa shi a addu’ar kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

Zuwa lokacin hada wannan labarin ‘yan bindigar ba su tuntubi iyalan Sarkin Fulanin ba.